Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Jagoran ya fara jawabinsa da nuna alhini dangane da waƙi'ar Ashura da kuma wafatin Imam Hasan Mujtaba (A.S). Sannan ya tunatar dangane da arba'in da ake fuskanta, da kuma jana'izar shahidin wannan al'umma, Shahid Sayyid Ali Khamene'i (RH).
Jagora ya jaddada cewa: "wannan taron, taro ne na tunawa da waƙi'ar da ta auku a ranar 28 ga watan Ramadan, 1436 daidai da 25 ga watan Yulin 2014. Shekaru 12 ke nan cif-cif a ƙidayar miladiyya."
Har wa yau, Jagora (H) ya tunatar da yadda aka soma muzaharar Ƙudus a Nijeriya, wadda aka fara gudanar da ita a Juma'ar farko bayan watan Ramadan a Zariya. Daga bisani kuma ta faɗaɗa zuwa sassan ƙasar nan sakamakon ƙaruwa da yawan jama'ar da ke halarta. Haka kuma ya yi bayanin yadda al'amarin Falasɗinu ya samu karɓuwa a tsakanin al'umma.
"Muzaharar Ƙudus na duniya nuna goyon baya ne ga al'ummar Falasɗinu wanda ƴan share wuri zauna ke musgunawa da zaluntar su tsawon shekaru fiye da 70",.
Ya ƙara da cewa: "Ana nuna cewa, ba a yadda da zalunci ba ne."
Har wa yau, a wani ɓangare na jawabinsa, Jagora ya tunatar da al'umma dangane da waƙi'ar da ta auku a rana irin ta yau. Ya ce, muzaharar Ƙudus ta wannan shekarar (2014), a nan ƙasar ne kawai aka auka mata. Ya ce: "wannan abin da ya faru bai ɓoyun ma al'umma ba. Ashe ba su dandara ba bayan shekara guda suka sake diran mana da nufin share kowa da kowa. Da ma manufar ke nan a waƙi'ar 25 ga watan Yulin 2014 sai ya ƙare kan mutum 34", ya nusasshe.
Dangane da masu afkawa muzaharar Ƙudus domin faranta ran Isra'iliyawa, Jagora (H) ya ce, abu ne mai sauƙi: "tunda mu muna nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Juma'ar ƙarshen watan Ramadan, sai ku ware watarana ba Juma'ar ƙarshen watan Ramadan ba sai ku goyi bayan Isra'iliyawa".
Jagora (H) ya jaddada cewa, ba za a ba mu tsoro da mutuwa ba: "ko ku yi harbi, ko kar ku yi harbi, za mu fito". Sannan ya ce, irin wannan taro, taro ne da ake tuna rayayyu da nassin Alƙur'ani. Ya ƙara da cewa: "idan aka ce an ga shahidi da ido, ba ma shakka", ya lurantar.
Jagora (H) ya ce, ko an kashe mutum ko kuma aka bar shi da rai, a ƙarshe dai zai mutu. Ya ce: "Abin alfahari ne a kashe ka a tafarkin Allah". Jagora ya nanata cewa, muna nan daram a wannan tafarki da aka kashe waɗannan shahidai. Ya ce: "muna nan daram a wannan tafarki da kuka bayar da rai a kai, ko a karrama mu, ko mu mutu a kan wannan tafarki, amma ba za mu sauya ba".
Dangane da masu kisan kai kuwa, Jagora (H) ya ce, su tuba, amma idan ba su tuba ba, za su yi hasarar duniya da lahira.
A ƙarshe, Jagora ya jaddada cewa: "wannan taro namu alama ce ta so, muna son waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu a wannan tafarki. Kuma kowannen mu hanƙoransa ke nan. Muna tunawa da wannan, muna ganin muna samun lada ne".
Bayan kammala jawabin, Jagora (H) ya gaisa da malamai, fastoci da sauran baƙin da aka gayyata zuwa taron, tare da iyalan Shahidai. Daga nan sai ya gudanar da ziyarar ƙaburburan Shahidan da ke kwance a Darur Rahma, sannan aka sallami al'umma.
Tun da farko, an fara taron da buɗe shi da addu'a, sannan aka yi karatun Alƙur'ani Mai Girma. Bayan haka aka gabatar da display daga lajanoni, tare da Faretin girmama Shuhada, sai kuma tamsiliyya da ta shafi waƙi'ar. Bayan kammala ziyarorin, Jagora (H) ya rufe taron da addu'a.
Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
11/safar/1448
25th/07/2026
Ra'ayinka